Za Mu Yi Dukkanin Mai Yiwuwa Wajen Magance Matsalar Tsaro A Katsina – Dikko Radda

Labarin dake shigo mana daga jihar Katsina na bayyana cewar tawagar yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar karkashin jam’iyyar APC Dr. Dikko Umaru Radda ta sauka a garin Safana.

Tawagar ta zagaya kafutanin mazabun karamar hukumar domin neman al’ummar yankin su zabe Jam’iyyar APC.

A yayin rangadin dan takarar gwamnan Dr. Dikko Umaru Radda ya tabbatar wa al’ummar Safana cewa lallai za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun tabbatar da dorewar Tsaro a Safana da ma jihar Katsina baki daya. Ya kara da cewa duk wani mai amfani da matsalar tsaro da kuma Danganta matsalar da siyasa to ba masoyin al’umma ba ne.

Ya yi kira ga Mutanen Safana da su fito kafutaninsu su zabi Jam’iyyar APC domin cigaba da samar masu da ababen more rayuwa na yau da kullum.

A yayi yakin neman zaben tawagar ta amshi sauran mutanen da suka rage wa Jam’iyyar PDP zuwa APC in da a yau aka amshi sama da mutane 8411 da suka wurgar da Lema suka rungumi tsintsiya domin amfana da romon Damakuradiyya.

Tawagar yakin neman zaben ta samu rakiyar ‘yan takarkari da kuma manyan jigajigan Gwamnati a kowane sashe na ciki da wajen jihar Katsina.

Labarai Makamanta

Leave a Reply