Za Mu Tabbatar Shari’a Ta Yi Aiki Akan Nnamdi Kanu – Ministan Shari’a

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis Ministan shari’a kuma babban lauyan Najeriya Abubakar Malami SAN yace ba za a yi dogaro da mayar da Nnamdi Kanu ba a matsayin dalilin sakin shugaban tsagerun kan zargin laifuka da yayi wa gwamnatin tarayya ba.

Ministan shari’an yayi bayanin cewa gwamnati na rike da Nnamdi Kanu ne kan dalilai hudu ba wai mayar da shi kasar da aka dauko shi ba kadai.

“Saki ko rashin sakin Nnamdi Kanu duk aikin doka ne a wannan lamarin. A wurin yanke hukuncin a sake shi ko kada a sake shi wani abu ne na daban. A duba doka, a duba jama’a da bukatar kasa, na uku a duba tsaro sannan a duba diflomasiyyar kasashe.

“A yanzu bari in fara da batun doka. Wannan mutum ne da aka bayar da belinsa kan wasu zarginsa da ake yi. Ya tsallake belin ya tsere, wani laifin ne wannan ya sake.”

“Na biyu kan batun tsaron kasa, wannan mutum ne da ake zargi da cin amanar kasa, assasa barna, kisan kai da sauran tarzoma da suka dinga barazanar ga tsaron kasa.

“Na uku kan batun diflomasiyyar kasashen ketare, wannan mutum ne da yayi amfani da wata kasa wurin kaddamar da farmaki kan kasarsa. “Toh wadannan dole a dube su kafin a san abin yi. Toh idan ta fannoni daban-daban aka gano abubuwan da suka hada da cin amanar kasa, kisan kai, tsallake beli da sauransu. Idan kayi nasara a kan abu daya yayin da ba a kammala sauran ba hakan ba zai sa a sake shi ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply