Za Mu Rataye Duk Wanda Ya Yi Mana Tu?in Ganganci A Zamfara – Matawalle

Gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun, ta yi alkawarin sake bullo da manyan hukunce-hukuncen kisa a kan direbobi masu tukin ganganci.

Babban daraktan na yada labarai na fadar gwamnatin jihar, Alhaji Yusuf Idris Gusau, ne ya bayyana hakan a takardar sanarwar da ya sanya ma hannu ya rabawa ‘yan jaridu a Gusau, babban birnin Jihar ta Zamfara.
Alhaji Yusuf ya kara da cewa, Gwamna Bello Matawallen Maradun, ya dau alwashin samar da sabuwar doka ga masu tukin ganganci ne a lokacin da ya jagoranci wakilan majalisar zartarwarsa da kuma shugabannin kungiyar BUA zuwa ziyarar ta’aziyya ga Sarkin katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, kan mutuwar mutane 15 daga masarautar sakamakon hadarin mota da suka yi a ranar Laraba da ta gabata.

Gwamna Matawallen Maradun, ya nuna alhininsa kan mutuwar mutane 15 da suka rasa rayukansu sakamakon tukin gangancin da wani direban babbar mota ya yi a ranar Larabar da ta gabata a kan hanyar Gusau zuwa Funtuwa.
Kuma nan take Gwamnan ya ba da gudummawar Naira miliyan 2 ga iyalan kowane mamacin wanda ke da mata. sai Naira miliyan 1.5 ga iyalan wadanda ba su da aure a cikinsu.
Gwamna Matawalle, ya ba da umurnin sanya dangin kowanne daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su a cikin alawus na Naira dubu hamsin kowanen su a kowane wata, ya ce za su ci gaba da kasancewa a cikin jadawalin albashin jihar har zuwa karshen wa’adin mulkin nasa.
Kuma gwamnatinsa za ta fara amfani da na’urar auna saurin gudu a kan manyan tituna da kuma auna nauyi a kan manyan motoci da kuma gwajin magunguna a kan direbobi domin kauce wa tukin ganganci da rikon sakainar kashi wanda galibi kan jawo asarar rayukan mutane.

Gwamna Matawalle ya ce, daukan wannan matakan sun zama dole, saboda direbobi da danginsu ba za su kara tunanin za su samu sauki idan direbobin suka kashe wani, domin a cewarsa rayukan ‘yan jihar sun fi kowane abu mahimmanci.
Ya kuma bayyana hadarin a matsayin babban abin tunawa tare da yin kira ga dangin mamatan da su dauki hakan a matsayin kadarar Allah, yana mai addu’ar Allah Ya karbi rayukan mamatan ya sanya su cikin Jannatul Firdausi.
Hakazalika, jagoran tawagar daga Kamfanin BUA, da diebansu ya yi sanadiyar asarar rayuka mutanen, Injiniya Aminu Suleiman ya ce, sun jajantawa gwamnati da masarautar Gusau, da mutanen jihar da dangin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin da ya rutsa da direban kamfanin, da fatan Allah ya jikansu kuma ya gafarta masu amin.

Related posts

Leave a Comment