Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Za Mu Magance Matsalar Tsaro Cikin Watanni Shida – Shettima

?an takarar mataimakin shugaban ?asa a inuwar APC, Sanata Kashim Shettima, yace idan suka ci za?en 2023, gwamnatin Bola Tinubu, zata kawo karshen matsalar tsaro cikin watanni shida zuwa shekara ?aya.

Shettima ya fa?i haka ne a wurin taron Bola Tinubu da ‘yan kasuwa a jihar Legas. “A tsakanin watanni Shida da shekara ?aya, shugaba na (Bola Tinubu) zai ha?a tawagar da zata kawo ?arshen wannan rashin hankalin,” inji shi.

Haka zalika a nasa jawabin, ?an takarar shugaban ?asa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matakan da zai ?auka na magance matsalar da ta hana ‘yan Najeriya zaman lafiya.

Tsohon gwamnan Legas ?in yace gwamnatinsa zata kara yawan dakarun soji, da jami’an tsaro a dukkanin hukumomin tsaro da ‘yan Sanda duk a wani ?angare na tabbatar da zaman lafiya.

“Za mu ?ara ?aukar mutane a hukumomin tsarom mu na Soji da ‘yan sanda. Dakarun mu zasu samu nagartaccen horo kan dabarun sadarwa, iya taku, da ?ara inganta sintirin sama da ?asa.”

“Ta wa?annan matakan da ma wasu, zamu gano da kuma murkushe tawagar she?anun nan ko ina suka ?uya. Ba zasu samu sa’ida ba har sai sun mi?a wuya ko a murkushe su.”

Exit mobile version