Za Mu Magance Matsalar Tsaro Cikin Watanni Shida – Shettima

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar APC, Sanata Kashim Shettima, yace idan suka ci zaɓen 2023, gwamnatin Bola Tinubu, zata kawo karshen matsalar tsaro cikin watanni shida zuwa shekara ɗaya.

Shettima ya faɗi haka ne a wurin taron Bola Tinubu da ‘yan kasuwa a jihar Legas. “A tsakanin watanni Shida da shekara ɗaya, shugaba na (Bola Tinubu) zai haɗa tawagar da zata kawo ƙarshen wannan rashin hankalin,” inji shi.

Haka zalika a nasa jawabin, ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matakan da zai ɗauka na magance matsalar da ta hana ‘yan Najeriya zaman lafiya.

Tsohon gwamnan Legas ɗin yace gwamnatinsa zata kara yawan dakarun soji, da jami’an tsaro a dukkanin hukumomin tsaro da ‘yan Sanda duk a wani ɓangare na tabbatar da zaman lafiya.

“Za mu ƙara ɗaukar mutane a hukumomin tsarom mu na Soji da ‘yan sanda. Dakarun mu zasu samu nagartaccen horo kan dabarun sadarwa, iya taku, da ƙara inganta sintirin sama da ƙasa.”

“Ta waɗannan matakan da ma wasu, zamu gano da kuma murkushe tawagar sheɗanun nan ko ina suka ɓuya. Ba zasu samu sa’ida ba har sai sun miƙa wuya ko a murkushe su.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply