Rahoton dake shigo mana daga Jihar Yobe na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta bada umurnin sanya suna sabbin dalibai milyan biyar cikin wadanda ake baiwa abinci kullum a makarantun gwamnati a fadin tarayya.
Ministar tallafi, walwala da jin dadin jama’a, Hajia Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan a Damaturu, jihar Yobe, yayin taron raba kayan girki ga ma’aikatan jihar.
Ministar, wacce ta samu wakilcin mataimakin daraktan Braille Library Bauchi, Hassan Maidugu, ya ce an yi wannan shiri ne don kawar da talauci da inganta rayukan al’umma.
Ya kara da cewa kawo yanzu mutum milyan tara ake ciyarwa kuma an dauki sama da masu girki 100,000.
A jihar Yobe kuwa, ya ce dalibai 103,929 ake ciyarwa kullu yaumin a kananan hukumomin jihar 17 a makarantu 248.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya samu wakilcin Bulau Aisami Geidam yace gwamnatinsa zata cigaba da baiwa wannan shiri karfin gwiwa.