Za Mu Kara Daukar Matasa Aikin N-Power Ba Da Jimawa Ba – Ministar Jin Kai

Rahotannin dake shigo mana daga Jos babban birnin jihar Filato na bayyana cewar Ministan jin ?ai da walwalar al’umma, Sadiya Farouq, ta ce ma’aikatarta zata samarwa matasa 13,823 a jihar Filato ?ar?ashin shirin NSIP, na gwamnatin tarayya ayyukan yi.

Minista Farouq ta yi wannan furucin ne a wurin taron rufe horarwa da kuma ba da jarin farko ga wa?anda zasu ci gajiyar shirin N-Skills a Jos ranar Talata.

Ministar wadda ta samu wakilcin daraktan sashin shugabanci na ma’aikatar, Ladan Haruna. Ta ce za’a samar da aikin ne ta hanyar N-power rukunin C.

A cewar Ministar jin ?ai an samu wannan cigaban ne biyo bayan amincewar shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, na ?ara fa?a?a shirin N-Power matasa da dama su amfana.

“Ina mai ?ara jaddada kudirin shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, na ya?ar talauci da shawo kansa da kuma shawo kan zaman kashe wando tsakanin matasa ta hanyar shirin NSIP.”.

“Mun fa?a?a ?angaren masu karatu da wa?anda ba su yi karatu ba na shirin N-Power domin samar da damarmaki ga matasa 13,823 a jihar Filato ka?ai a rukunin C.”

“Hakan ya biyo bayan samun nasarar gama cire matasa 11,505 a rukunin A da B. Bisa umarnin shugaban ?asa zamu nunka wa?annan damarmaki ga matasa.”

Related posts

Leave a Comment