Za Mu Hukunta Wadanda Suka Shigo Da Gurbataccen Mai – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce dole ne wadanda suka shigar da gurbataccen man fetur din da aka rinka sayar wa a kasar a kwanakin nan su yi bayani ko su fuskanci hukunci.

Shugaban ya bayar da umarni ga dukkanin hukumomin da abin ya shafada su dauki duk matakin da ya dace da dokar kasar, domin tabbatar da kare jama’a masu amfani da kayayyaki daga masu algus da zalunci.

Kakakin shugaban, Mallam Garba Shehu, ne ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar Alhamis din nan.

A sanarwar shugaban ya ce kare muradun jama’a abu ne da gwamnatinsa ta ba fifiko, kuma a shirye yake ya dauki dukkanin matakan da suka wajaba ya kare mutane daga gurbatattun abubuwan da za su cutar da su.

Related posts

Leave a Comment