Za Mu Hada Hannu Da Google Wajen Samar Da Ayyuka Miliyan Guda A Najeriya – Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce a shirye gwamnatinsa take wajen mara wa babban kamfanin fasaha na Google baya don samar da ayyukan yi miliyan guda a ƙasar.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da mataimakin shugaban kamfanin Mista Richard Gingras ya ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake ya fitar, Shugaban na Najeriya ya ce Najeriya na da matasa masu basira da fasaha, waɗanda koyaushe a shirye suke wajen koyon sabbin abubuwa musamman a wannan zamani na bunƙasar fasahar zamani.

Yana mai cewa kamfanin google na da dukkan abubuwan da matasan Najeriya ke buƙata don bunƙasa fasaharsu.

“Ina farin ciki cewa Google a shirye yake ya yi aiki da mu. kun amsa kiranmu wajen samar wa matasanmu sabbin ayyukan fasahar zamani. Kuna mara wa yunƙurinmu baya na bunƙasa sabbin hanyoyin tattalin arziki na zamani. A shiye muke mu yi aiki da ku kan yunkurinku na amar da ayyukan yi miliyan guda ga matasanmu”, in ji shugaban na Najeriya.

Ya ƙara da cewa “Za mu ba ku duk goyon bayan da kuke buƙata domin cika wannan buri naku”.

Najeriya na da miliyoyin matasa marasa aikin yi a ƙasar wadda ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afirka

Labarai Makamanta

Leave a Reply