Za Mu Fidda Mutum Miliyan 100 A Talauci Nan Da Shekaru 10 – Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari yasha alwashin tabbatar dacewa, muradun tsamo miliyan 100 daga ƙangin talauci an cimma shi a shekaru 10 masu zuwa.

Shugaban Ƙasar ya bayyana haka a jawabin da yiwa ƴan kasa na murnar cikar Najeriya 61 da samun ƴancin kai a Villa dake Abuja.

Acewar sa ta la’akari da nasarorin da aka cimmawa a shirye-shirye tallafawa, ya amince da ƙarin ɗaukar masu amfana da shirin N-Power daga dubu ɗari 500,000 zuwa miliyan 1,000,000, daga cikin haka mutane dubu 510,000 sun fara shirin, a yayinda ake cigaba da zaɓar saura mutane dubu ɗari 490,000 waɗanda zasu amfana da shirin wanda yake gudana a halin yanzu.Buhari

Ya ƙara dacewa, shirin ciyar da Ɗalibai ƴan makaranta wanda aka ƙaddamar a faɗin jahohi 35 da babban birnin tarayya Abuja, an ɗauki sama da mata dubu 103,000 da aka ɗauka, domin dafa abinci a ƙarƙashin shirin, a yayinda kimanin yara miliyan 10 ake ciyar wa a faɗin ƙasar.

Shugaba ya kuma bayyana cewa ya bada umarnin a ƙara yawan mutanen da ake baiwa kuɗaɗen tallafi ya zuwa miliyan 1.

Labarai Makamanta

Leave a Reply