Za Mu Fallasa Masu ?aukar Nauyin Ta’addanci Muddin Basu Bari Ba – Masoya Buhari

Kungiyar Magoya bayan Shugaban masa, Muhammadu Buhari me sunan #ISTANDWITHBUHARI ta baiwa masu daukar nauyin ‘yan Bindiga wata daya su daina ko ta tona Musu Asiri.

Mr. Efeanyi Ezedinma wanda shine Shugaban kungiyar ya bayyana haka a Abuja a ganawar da yayi da manema labarai, Ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa anawa Gwamnatin tarayya Zagon kasa, kan magance matsalar tsaro da take yunkurin yi. Yace, suna da takardun bayanan sirri da suka fadi sunayen mutane masu daukar nauyin ‘yan ta’adda hadda ma guraren da suke zaune a cikin kasarnan.

Yace sun basu nan da wata daya su daina ko su tona Musu Asiri. Yace maganar gaskiya Najeriya ba zata rabu ba kuma Shugaban kasa, Muhammadu Buhari na nufin kasar da Alheri

Related posts

Leave a Comment