Za Mu Ɗaure Duk Wanda Ya Ƙara Zagin Shugabannin Najeriya – NBC

Hukumar lura da kafafen yada labarai a Nijeriya NBC, a ranar Alhamis ta ce za ta fara hukunta duk tashar watsa labaran da ta sabawa dokokinta.

Ta gargadi kafafen watsa labarai cewa su fahimci dokoki da ka’idojin sana’ar.

Diraktan hukumar NBC na jihar Legas, Chibuike Ogwumike ya bayyana hakan a takardar da aikewa manema labarai.

Yayin bayyana wani sashen dokokin, Chibuike yace sashe na 3.1 ya bayyana cewa “Babu tashar watsa labaran da aka amince ta baiwa wani dama ingiza mutane zuwa aikata wani laifi, da zai iya kai ga rabuwar kai da kuma wanda ya kunshi kalaman batanci kan wani mutum ko kungiya.

Sashe na 3.1.19 yace: “Ba’a amince kafar watsa labarai ta watsa sakon da ke cin mutuncin al’adunmu.

Ya kara da cewa: Sakamakon bincike ya nuna cewa kwanakin nan, wasu kafafen yada labarai sun daina aikinsu na tantance kalaman mutanen da suka gayyata shirye-shiryensu inda ake zagin shugabanni da masu mulki a fili.

Cin mutuncin shugabanninmu da manyamu da kalaman zagi ya sabawa al’adarmu. Muna ganin girman shugabanninmu kuma hakan ne al’adarmu.

Zagi da cin mutuncin shugaban kasa, gwamnoni, yan majalisar da sauran shugabanni ya sabawa al’adarmu.

A bangare guda, hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa (NBC) ta ci tarar wani gidan radiyo da ke jihar Legas Naira miliyan biyar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply