Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Za A Yi Yajin Aiki Mafi Muni A Najeriya Idan… – Ƙungiyar Kwadago

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar kwadago ta kasa ba ta yi na’am da shawarar da kungiyar gwamnonin Najeriya ta bada na tsaida farashin fetur a tsakanin N380 da N408 ba. Inda ta bayyana cewar akwai neman takalo rigima da rashin tausayin al’umma a matsayar da kungiyar gwamnonin ta dauka na cewa a daina biyan tallafin Mai.

Idan aka yi la’akari da halin da ‘yan Najeriya ke ciki, musamman ma’aikata, kungiyar kwadago ta ce bai dace a bada shawarar a kara farashin litar mai ba gaba ɗaya matukar akwai tausayi da Imani.

Kwamitin Gwamna El-Rufai ya na so litar fetur ta kai N408 NLC ta ce: Ko da karin 1% aka yi a kan abin da ake saida albarkatun mai a yanzu musamman fetur, hakan zai jawo mu janye hannunmu, ma’aikata a fadin kasar nan su tafi yajin-aiki ba tare da an sanar da lokacin dawo ba.”

A wata takarda da kungiyar Ƙwadagon ta fitar bayan zaman da ta yi a ranar Talata a Abuja, kungiyar ta yanke shawarar ta kai wa gwamnati kukanta, dangane da ake ciki da abin da zai biyo baya muddin aka yi gigin ƙara farashin man.

Kungiyar Kwadagon ta rubuta takarda zuwa ga gwamnatin tarayya, ta sanar da ita game da halin da ma’aikata suke ciki, da matakin da suka dauka a kan batun.

Shugaban Kungiyar Kwadago na kasa, Ayuba Wabba, da sakatarensa, Ismail Bello sun sa hannu a matsayar da aka dauka, suka tabbatar da rashin goyon bayan karin kudin mai gaba ɗaya.

Har ila yau, Ƙungiyar Kwadago ta ce ba ta cikin wata yarjejeniya da gwamnati kan maganar tsaida farashin mai, ta ce zaman da aka shirya za ayi a kwanaki bai yiwu ba.

An ruwaito cewa Ƙungiyar Kwadagon ta sanar da sauran takwororinta su fara shirya wa tafiya yajin-aiki, idan gwamnati ta karbi shawarar Gwamnonin, ta kara farashin fetur.

A kwanakin baya, kungiyar gwamnonin Najeriya NGF karkashin Gwamna Kayode Fayemi, ta kafa kwamiti na musamman domin duba batun cire tallafin mai ƙarkashin Gwamnan Jihar Kaduna El Rufa’i, inda ya amince da yin ƙarin farashin Man.

Exit mobile version