Za A Yi Wa Dakarun SARS Gwajin Ƙwaƙwalwa – Shugaban ‘Yan Sanda

Shugaban rundunar ‘yan sanda, Mohammed Adamu a ranar Talata ya umurci gaba daya jami’an da ke a sashen dakile fashi da makami SARS da su je shelkwatar rundunar da ke Abuja domin bincikar ƙwaƙwalwar su.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an idan sun je Abuja, za ayi masu gwajin kwakwalwa a shirye shiryen yi masu horo don rarrabasu zuwa wasu sashe sashe na rundunar.

Da ya ke bayyana hakan a cikin wata sanarwa, Frank Mba, jami’in hulda da jama’a na rundunar, ya ce: “Sabon sashen tuntuba da bayar da shawarwari na rundunar (PCSU) zai gudanar da binciken kwakwalwar.

“Sashen zai kula da lamarin horaswa, binciken kwakwalwa da kuma bayar da shawarwari ga jami’an ‘yan sanda da aka turasu ayyukan dakile ta’addanci.”

Sashen, wanda ya ke jingine da bangaren kiwon lafiya na rundunar kuma karkashin kulawar jami’in lafiya, na da ma’aikatan kwakwalwa, ilimin rayuwa, likitanci, malaman addinai, jami’an hulda da jama’a da sauransu.

A wani ci gaban kuma, Shugaban ‘Yan sandan ya samar da sashen jami’an da suka kware a sarrafa makamai da fada (SWAT) da zai cike gurbin korarren sashen jami’an SARS.

Dakarun wannan sabon sashen za su samu horo da kuma jarabawar kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya gudanar da wannan muhimmin aiki. Za su fara samun horo a sansanonin horar da jami’an rundunar ‘yan sanda daban daban da ke fadin kasar, a mako mai zuwa.

Za a horas da jami’an rundunar da ke a shiyyoyin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu a sansanin horas da jami’an na Nonwa-Tai, jihar Rivers. Haka zalika, za a horas da jami’an rundunar ‘yan sandan shiyyar Arewa da Kudu maso Yamma a kwalejin horas da ‘yan sandan sintiri da ke Ende, jihar Nasarawa da kuma wacce ke Ila-Orangun, jihar Osun.

Labarai Makamanta

Leave a Reply