Za A Yi Ruwan Harsasai Yau A Yobe – Rundunar ‘Yan Sanda

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Yobe tana sanar da jama’ar dake cikin garin Damaturu fadar Gwamnatin jahar Yobe musamman wadanda suke hanyar Gashua cewa a yau Talata 15 ga wannan wata na Satumba da misalin karfe bakwai na safe za su yi gwaje-gwajen makaman su na bindigogi.

Don haka suke sanar da jama’a kar su tsorata su dauka wani abu ne. Kuma suna kira ga jama’a dan Allah su sanar da mutanen da basu sani ba.

Yin gwaje gwajen makamai ga jami’an tsaro a Najeriya ba sabon abu ba ne, sai dai a duk lokacin da za’a yi gwajen gwajen, jama’a na shiga cikin fargaba da ruɗani, wannan shine dalilin da ya sanya, hukumomin tsaron ke ƙoƙarin sanar da jama’a, a duk lokacin da gwajin ya tashi.

Jihar Yobe da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya dai na ɗaya daga cikin jihohi da ke fuskantar hare hare na kungiyar Boko Haram a Najeriya, kasancewar jihar na makwabta da Jihar Borno, Hedkwatar Boko Haram.

Labarai Makamanta