Za A Yi Jana’izar Mutane 51 Da ‘Yan Bindiga Suka Hallaka Zamfara

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar nan gaba a yau ne za a yi jana’izar ?arin wasu mutane da ‘yan Bindiga suka kashe bayan wani mummunan artabun da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

Wani ganau ya fa?a wa BBC cewa ya zuwa marecen Laraba, sun ?irga mutum 51 da aka kashe daga ?auyukan gundumar Magami daban-daban.

‘Yan fashin daji sun auka wa mutane ne lokacin da suka yi yun?urin kai ?auki ga mutanen ‘Yar Doka, wa?anda wasu bayanai ke cewa sun koma gida daga gudun hijira, kwana ?aya kafin wannan ?azamin hari.

Rahotanni sun ce har zuwa daren jiya mutane na ci gaba da tsere wa ?auyukan yankin zuwa gudun hijira a Magami mai nisan kimanin kilomita 18.

Shaidu sun ce cikin mutanen da aka kashe akwai a?alla mutum 20 daga ?auyen Ruwan Dawa, sai goma na Kangon Fari Mana, shida daga Madaba, Arzi?in ?a ma mutum shida, Mai Kogo da Mai Aya-aya da Mai Rairai kowanne mutum biyu da Gidan Maza da Kunkelai mutum ?ai-?ai.

Wannan shaida daga Kangon Fari Mana ya ce ‘yan fashi sun shafe kimanin awa bakwai suna harbe-harbe.

Bayanai sun ce mutanen ?auyen ‘Yar Doka da suka nemi ?auki daga ma?wabtansu, sun koma gida ne kwana ?aya kafin harin, don ganin ko akwai halin noma gonakinsu.

Sai dai a cewar mazaunan yankin ‘yan fashin daji sun ci alwashin cewa ba za a yi noma ba a fa?in gundumar Magami, kuma suna tsammanin wannan ?uduri ne ya sanya su yin gangami don sake auka wa ?auyen ‘Yar Doka.

A safiyar nan ne ake jana’izar mutanen Kangon Fari Mana su goma a garin Magami.

Mutanen ?auyen sun ce ba za su iya yi wa ‘yan uwan nasu sutura ba a can saboda fargabar maharan za su dawo a kowanne lokaci.

Baya ga mutanen da aka kashe, wani shaida ya ce an kai mutum 11 da aka jikkata babban asibitin Magami inda suke ci gaba da samun kulawa.

Sun ce ba su da tabbaci ko an samu asarar jin rauni ko mutuwa a ?angaren ‘yan fashin daji, don kuwa sau da yawa sukan kwashi mutanensu ne su tafi da su.

Sun koka da rashin samun ?aukin jami’an tsaro, wa?anda suka ala?anta da lungun yankin nasu da kuma ?arancin kayan aikin jami’an tsaro. Sun ce hatta jirgin ya?in da ya je daga bisani bai iya fatattakar maharan ba.

Related posts

Leave a Comment