Za A Yi ?azamar Zanga-Zanga Muddin ASUU Ta Cigaba Da Yajin Aiki – ?alibai

Kungiyar daliban Najeriya ta yi kira da babbar murya ga ?aliban Najeriya cewa su shirya afkawa cikin wata ?azamar Zanga-Zanga muddin Kungiyar malamai masu koyarwa a jami’o’i ASUU suka sake fadawa yajin aikin a Najeriya.

Shugaban kungiyar ?aliban NANS, Sunday Asefon, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da manema labarai da yayi a ranar Alhamis ?in nan a birnin tarayya Abuja.

Kwamared Asefon ya ce abun kunya ne da takaici yadda ASUU take sake barazanar shiga sabon yajin aiki bayan ?ata wa daliban Najeriya watanni tara a banza, da mayar musu da hannun agogo baya.

“Wannan abun kunya ne a garemu da ASUU tace ta janye yajin aiki amma da sharadi. Idan suka koma aiki da sharadi, mu ma za mu tsaya da shirin mu na fara zanga-zanga.

“Amma idan suka koma yajin aiki, za mu hau tituna tunda yaren da kadai suke ganewa kenan, shi za mu yi musu kuma muna tabbatarwa jama’a za’a fuskanci ?azamar Zanga-Zanga ta nuna fushi da fusatar mu”.

An ruwaito cewa shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi, a ranar Laraba a Abuja ya sanar da janye yajin aikin da aka kwashe watannin tara ana yi amma da sharadi.

Ogunyemi wanda yace an janye yajin aikin a ranar Alhamis, 24 ga watan Disambano 2020, ya tabbatar da cewa kungiyar za ta sake komawa yajin aikin matuukar gwamnati ta kasa cika alkawarinta.

Related posts

Leave a Comment