Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva ya gargadi ‘yan Nijeriya da su kasance cikin shirin jure wahalar karin farashin mai yayin da farashin danyen mai ya haura sama da $60 a kowace ganga.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin Inganta Kudin Najeriyar a ranar Talata, Sylva ya ce ba tare da samar da tallafi a cikin kasafin kudin 2021 ba, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), ba zai iya ci gaba da daukar nauyin da ke kasa-kasa ba.
A halin yanzu, farashin man fetur ya kai N160 zuwa N165, farashin da aka sanya lokacin da danyen ya yi sama da $43 a kowace ganga, watanni hudu da suka gabata.
A cewar Ministan, yayin da kudaden shigar da gwamnati ke samu ya inganta ta hanyar hauhawar farashin danyen mai, ba za a iya damunta cikin biyan tallafi ba.
Ya ce: “Tunda muna inganta komai, NNPC na bukatar kuma tayi tunani game da inganta farashin kayan saboda kamar yadda kowa ya sani farashin mai yana inda yake a yau, $60.
“A matsayinmu na kasa, bari mu dauki fa’idar karin farashin danyen mai kuma ina fatan za mu kasance a shirye mu dauki dan karamin ciwo a kan karin farashin kayayyakin”, in ji shi.