Za A Na?a Tsoffin Shugabannin Tsaro Mu?amin Jakadu

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya tura sunayen tsofaffin hafsoshin tsaro zuwa Majalisar Dokoki ta kasa, inda ya bukaci a tantance su domin a ba su mukamai a matsayin Jakadun Najeriya a kasashen Ketare.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai ta kafafen zamani, Bashir Ahmad, ya bada wannan sanarwa a shafinsa na Twitter da yammacin wannan rana ta Alhamis.

Bashir Ahmad ya bayyana cewa shugaban kasa ya aika takarda zuwa ga shugaban majalisa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan game da batun tatance tsoffin Shugabannin tsaron matsayin Jakadu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya dogara ne da sashe nan a 171 (1), (2) (c) da karamin sashe na (4) na kundin tsarin mulki wajen bada mukaman.

Kamar yadda hadimin shugaban kasar ya bayyana dazu nan, an aika sunayen mutane biyar ne zuwa ga majalisar dattawan a yau ranar Alhamis.

Ga sunayen kamar haka: Janar Abayomi G. Olonisakin (Rtd), Laftana Janar Tukur Y. Buratai (Rtd), da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (Rtd). Haka zalika Air Marshal Sadique Abubakar (Rtd), da Air Vice Marshal Mohammed S. Usman (Rtd).

Related posts

Leave a Comment