Masarautar Kano ta sanya ranar 28 ga watan Mayun nan a matsayin ranar da za ta na?a tsohon Chiroman Kano, Murabus wato Lamido Sunusi Ado Bayero a matsayin Wamban Kano.
Tun da farko shafin masarautar Kano na facebook ne ya wallafa sanarwar nadin na Lamido Sunusi Ado Bayero.
“Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai nada dan uwansa kuma tsohon Chiroman kano murabus Alhaji Sunusi Ado Bayero, sarautar Wamban Kano, ranar juma’a 28/5/2021 da misalin karfe 10:00 na safe a fadar masarautar Kano. Allah ya sanya alkhairi Amin. Allah ya taimaki sarki ran sarki ya dade”
Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2015 majalisar masarautar Kano ta sauke Alhaji Lamido Ado Bayero daga sarautar Ciroma, sakamakon rashin mubaya’a ga tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II.
Alhaji Lamido Ado Bayero, shi ne mutumin da ya yi takarar neman sarautar Kano da tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, bayan mahaifinsa Alhaji Ado Bayero ya rasu.
Haka kuma tun da ya rasa kujerar Sarkin Kanon, majalisar masarautar ta ce bai yi mubaya’a ga sabon Sarkin ba.