Za A Kashe Biliyoyi Wajen Yi Wa Fadar Shugaban Kasa Kwaskwarima

Rahotanni sun tabbatar da cewa an ware Naira biliyan 5.3 da nufin yin wasu ‘yan gyare-gyare da kwaskwarima a ofisoshi da gidajen da ke cikin fadar Shugaban Kasa Aso Villa.

Wannan duk ya na cikin abin da aka shirya a kundin kasafin kudin shekarar 2021 wanda shugaba Muhammadu Buhari ya mikawa majalisa a makon jiya.

Wadannan kudade su na kan layin ERGP 7102245 annual routine maintenance of mechanical/electrical installations of the Villa a kundin kasafin badi.

Bayan N4, 854, 381, 299 da za a batar wajen aikin wuta, fadar shugaban kasar za ta ci N153, 693, 262 a gyaren dakuna da N5, 244, 027, 241 a kan ofisoshi.

Naira miliyan 5.2 za su tafi wajen gyaran injin janareto a shekara mai zuwa. Bayan haka gwamnatin tarayya za ta batar da Naira miliyan 45 wajen mai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ware Naira miliyan 274 domin biyan kudin shan wutar lantarki da Naira miliyan 67.1 na hawa shafukan yanar gizo.

Gwamnatin tarayya ta yi wannan lissafi ne a lokacin da ta ke kukan rashin kudi, har ma ana tunanin tattalin arzikin Najeriya zai iya durkushewa a shekara mai zuwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply