Za A Iya Shahara A Waƙa Ko Ba Daɗin Murya – Ali Jita

Daya daga cikin manyan mawakan masanaantar Kannywood dake samar da wasannin harshen Hausa, mawaki Ali Isah Jita, ya ce ba dole bane sai muryar ka tana da dadi zaka iya zama Shahararren mawaki.

Ya ce zai iya lissafa mawaka da dama wadanda muryoyin su basu da dadi amma sun shahara a fagen waka kuma ana ci gaba da damawa da su har yanzu.

Ali Isah Jita, abun da ake so da mawaki ko waka, fahimtar da masu saurare sakon da waka take dauke da shi, ko kuma fahimtar da su sakon waka.

Da yake tattaunawa da wakilin mu ta na’ura, Ali Jita, ya ce akwai mawakan Hausa da dama da muryar su bata da dadi amma kuma ana son wakar su a saboda haka ne ma suka shahara.

Idan baku manta ba Mawaki Ali Isah Jita, bai cika yin wakokin da ake sakawa a shirye-shiryen Kannywood ba hasalima yafi mayar da hankali a wakokin Mata, wakar Aure wani lokaci ma har da Wakar Siyasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply