Hukumar Sa-ido da Hana Sauti Gurɓata Yanayi (NESREA) ta bayyana cewa ta na da ƙarfin ikon gurfanar da duk wani coci-coci, masallatai da masana’antu masu yin abin da ya kira “damun jamai da ƙarar da ta wuce ƙa’ida’ maka su kotu domin a hukunta su.
Babban Daraktan NESREA, Aliyu Jsuro ne ya bayyana haka a wata ganawar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ranar Lahadi a Abuja.
Aliyu ya bayyana cewa jama’a da dama na kai ƙorafe-ƙorafen yadda wasu wuraren ibadu da masana’antu da gidajen kaɗe-kade ke damun su da ƙara.
Sai ya ce bai kamata ana ƙure ƙarar lasifika a wuraren ibada ko kaɗe-kaɗe ba, saboda ana shiga haƙƙin mutane, tsirrai da dabbobi.
“Idan ƙara ta yi yawa, ta na yi wa tsirrai, dabbobi da mutane illa.
“Matsawar ana cika wa mutum kunnuwa da ƙara, to lafiyar za ta tawaya har ya samu hawan jini da wasu cututtuka.”
Ya ƙara da cewa shi ya sa hukumar su ke bi su na wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin rage ƙarar na’urori irin su lasifika da sauran mu.
“Za mu ci gaba da bi ana wayar wa masu wadannan wurare kai. Mu kan aika da takardun gargaɗi sau biyu. Na uku kuwa dama kawai gurfanarwa ce a kotu.” Inji shi.
Idan ba a manta ba, a cikin watan Yuni ɗin nan ƙasar Saudiyya ta sa dokar hana kunna lasifika a masallatan ƙasar fiye da 30% bisa 100 % na ƙarar lasifika ɗin.