Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a baiwa ‘yan Nijeriya milyan 24, kowannensu naira dubu 5000 na tsawon watanni shida daga cikin kokarin gwamnati mai ci na fitar da mutane daga kangin talauci.
Ma’aikatar harkokin agaji da magance annoba ce ta bayyana hakan a ranar Talata, 19 ga watan Janairu.
Da take Karin haske a kan lamarin a Abuja ta wani jawabi daga hadimarta Nneka Anibeze, ministar walwala, Hajiya Sadiya Farouq, ta ce shirin zai gano tare da yi wa mutanen da ba a yiwa rijista a baya ba rijista domin basu tallafin, jaridar Punch ta ruwaito.
A halin yanzu dai ‘yan Najeriya sun zuba idanuwa domin ganin ko wannan romon bakan zai zamo romon dimokradiyya.