Za A Cimma Nasara A Katsina Karkashin Gwamna Dikko Radda- Sabi’u Mahuta

An bayyana cewar da akwai kyakkyawar fata da samun nasara a jihar Katsina ƙarkashin jagorancin Gwamnan Jihar Dr Malam Dikko Umar Radda.

Bayanin haka ya fito ne daga wani jigon jam’iyyar APC a Jihar Alhaji Sabi’u Sa’idu Mahuta lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai jim kadan bayan kammala rantsar da Kwamishinonin jihar Katsina guda 20 da masu bada shawara 18 da ya gudana a garin Katsina.

Mahuta wanda shine daraktan Kamfanin mai na AA Rano kuma Sardaunan Danejin ya ƙara da cewar jumaar da za ta kyau tun daga Laraba ake ganeta tun lokacin da Gwamna Radda ya bayyana kudirorin da yake da su na ciyar da jihar Katsina ya tabbatar da cewa babu shakka an ba wa wuka nama.

“Ina son in sanar daku cewa a lokacin da Dr Radda ke yaƙin neman zaben zama gwamna a wannan lokacin ba na tare da tafiyarsa, amma daga baya da na fahimci cewa da mai kama ake ƙota sai na gaggauta barin inda nake na dawo cikin tafiyarsa”.

Dangane da tsarin da sabuwar gwamnatin Katsina take da shi dashi na ciyar da jihar gaba kuwa, Mahuta ya bayyana cewa ai tun ran gini ran zane domin ayyukan raya ƙasa da aka yi a baya cigaban su ne za a samu a yanzu saboda haka babu shakka jihar Katsina za ta zartar tsara.
“Ina tabbatar muku da cewar tsare-tsaren Gwamna Dikko Radda a fili suke kuma shakka babu akwai kyakkyawar fata da samun nasara ga jama’ar jihar Katsina gaba daya”.

Dangane da sabuwar majalisar zartawar da aka rantsar kuwa Dr Mahuta yace bisa ga zubin waɗanda Gwamna Radda ya zaɓo babu shakka an zaɓo waɗanda suka cancanta kuma hakika jihar Katsina ta ɗauki saiti”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply