Za A Cigaba Da Saurarar Shari’ar Zakzaky A Karshen Wata

Kotun dake sauraron karar shugaban kungiyar Shi’a ta IMN, Ibrahim Al-Zakzaky da mai dakin sa Zeenatu ta ?age zaman shari’ar zuwa 31 ga watan maris da muke ciki.

A zaman kotun Wanda aka shafe kimanin awa shida ana shari’a a karkashin jagorancin mai shari’a Gideon Kurada ta dage zaman kotun zuwa Karshen wannan watan.

Babban sakataren ma’aikatan shari’a na jihar kaduna kuma daya daga cikin lauyan gwamnati, Chris Umar ne ya bayyana wa manema labarai hakan jim kadan bayan kammala zaman kotun.

Ya kara da cewa sun gabatar da shaidu 14 a gaban kotun ciki har da sojoji 2, da jami’an yan sanda na ciki guda 1 da yayi ritaya da wasu mutane. kuma sun bada gamshashshen shaidar su kan shari’ar da akeyi tsakanin gwamnati da shugaban kungiyar IMN, Ibrahim Alzakzaky.

Shima babban lauyan najeriya Femi Falana da ke kare Ibrahim Alzakzaky ya bayyana cewar an gabatar da wasu shaidu gaban kotun Inda suka kawo shaidar faifan bidiyo, bindigar gargajiya da akafi sani da baushe, layukan waya da dai Sauran su.

Kuma Suma za su fara bayyana wa kotun sahihan bayanai na kariya akan shaidar da aka bayar kan Wanda suke karewa a zaman kotun na gaba da za ayi a Karshen wannan watan.

Idan ba a manta ba, an fara wannan Shari’ar ne tsakanin Zakzaky da gwamnatin jihar Kaduna tun a ranar 18 ga watan nuwanbar shekarar 2020

Related posts

Leave a Comment