Zaɓen Ondo: Muna Jiran Saƙon Taya Murna Daga PDP – Buni

Jam’iyya mai mulki ta APC ta ce har yanzu tana zuba idon samun sakon taya murna daga jam’iyyun siyasa musamman daga wajen PDP, a nasarar da ta yi a zaben ranar Asabar na Gwamnan jihar Ondo.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni, ne ya fadi hakan a wata hira da manema labarai a sakatariyar Jam’iyyar na kasa, a Abuja, a ranar Litinin.

Buni ya ce: “masu iya magana sun ce, yana da kyau mayar da alkhairi da alkhairi, kuma kamar yadda muka taya PDP murna a zaben Edo, muna jiran ganin sakon taya murna daga PDP da sauran jam’iyyun siyasa a nasarar da muka samu a zaɓen Ondo.

“Ta hakan, za mu karfafa zabe a Najeriya, maimakon mayar da zabe abin a mutu ko ayi rai.”

Amma da yake martani, babban Sakataren PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya bayyana tsammanin Buni a matsayin rashin tunani.

Ologbondiyan ya ce: “abun dariya ne cewa Gwamna Buni na barar samun yardarmu kan zaben duk da yana sane da cewar akwai tangarda a tsarin da ya kai dan takarar jam’iyyarsa ga nasara.”

“Maimakon rokar sakon taya murna daga PDP, kamata yayi ace Buni ya yi magana kan satar kudin da ake yi don daukar nauyin jam’iyyarsa ta hanyar siyan kuri’u a hannun ‘yan Najeriya da ke fama da radadin karin farashin man fetur, da kuma rashawa da ake a fannin mai karkashin APC.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply