Jam’iyyar PDP ta kadu da wannan hukuncin da kotun koli ta yanke akan karar da aka shigar akan zaben gwabnan da aka gabatar a jahar Kogi a 2019.
Jam’iyyar tace tayi mamakin da hukuncin kotun kolin, da kuma na kotun daukaka kara , mutanan Kogi da mafi aka sarin yan Najeriya basuji dadin wannan hukuncin ba ,wanda kowa yasan rashin adalcine ,duk da magudin da akayi, tashin hankali da kashe kashen da akayi a zaben.
Sanarwan ta bakin
Kola Ologbondiyan
Sakataren watsa labarai tacw Tabbas,wannan hukuncin zai kashe wa mutane gwiwa duk da kashe kashen da kuma rashin bin ka’idojin da akabi wajen samun nasara,Wanda duk sun samu a zaben Kogi amma akayi wannan hukuncin.
Amma dai,a matsayin mu na jam’iyya mai bin doka,muna Kira ga mutanan Kogi da kuma sauran yan Najeriya,su Kwantar da hankalin su,da yardar Allah za’a samu gyara akan harkar zabe a kasar nan .
Jam’iyyar mu tana kara mika jajenta da ta’azziyyarta ga mutanan da APC suka kashe a zaben gwabnan da aka gudanar a watan Nuwamba na 2019.
PDP tace tana kara godewa mutanan Kogi akan juriyar da sukayi wajen wannan shari’ar har zuwa karshe.wannan sadaukar war abun a jinjinane kuma ya nuna mutane zasu iya tsayawa wajen kare hakkinsu har zuwa karshe.
Jam’iyyar mu zata cigaba da kare martabar mutanan Kogi da kuma kalubalantar wannan gwabnatin da aka kakaba musu a Kogi.
Muna Kira ga mutane da kada wannan hukuncin yakar ya musu karfin gwiwa su cigaba da zama cikin hadin kai, su zama mutanan kirki,domin samun damar dawo darajar kasar nan.