Zaɓen Edo: Za Mu Yi Amfani Da Rajistar 2019 Ne – INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta yi amfani ne da rajistar masu zaɓe ta 2019 wajen gudanar da zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Edo.

Ya ce za a yi hakan ne saboda annobar korona, wato COVID-19.

Kwamishinan hukumar zaɓen wanda ke da zama a jihar, Dakta Johnson Alalibo, shi ne ya bayyana haka a wani zaman tattaunawa da aka tsakanin hukumar da ƙungiyoyi masu zaman kan su su sama da 70 a Abuja.

A cewar Alalibo, akwai jimillar masu zaɓe da aka yi wa rajista su 2,210,534 a Edo, yayin da an karɓi katin zaɓe guda 1,726,738.

Ya ce: “Hukumar ta ɗage karɓar katin masu zaɓe tare da yi wa masu zaɓe rajista saboda annobar cutar korona. Saboda haka, za mu koma ga abin da mu ka yi amfani da shi a babban zaɓen 2019, shi za mu yi amfani da shi.

“Tun daga lokacin da aka bayyana jadawalin ranakun zaɓen Edo, ayyuka daban-daban da su ka danganci zaɓen sun lulluɓe hukumar, kama daga sa ido kan zaɓuɓɓukan share fage na jam’iyyun siyasa zuwa buga fom-fom masu ɗauke da sunayen ‘yan takara.

“Mun karɓi wasu daga cikin kayan aiki kuma har yanzu mu na karɓar su tare da rarraba su a Yankunan Ƙananan Hukumomi.

“Mun samu ƙarancin na’urorin karanta katittikan zaɓe masu ƙwaƙwalwa, mun buƙata kuma an kawo mana daga wasu jihohin. Mun gama auna na’urorin tare da buga rajistar masu zaɓe.’’

Alalibo ya ƙara da cewa shi ma aikin horas da ma’aikatan zaɓe da jami’an tsaro, wanda aka raba a matakai uku, an kammala shi.

Ya ce an gama tsara yadda za a taimaka wa naƙasassu su yi zaɓen, kuma an yi masu isasshen tanadi.

Ya ce akwai shirye-shiryen faɗakarwa da ake yi yanzu a rediyo da sauran yekuwa don ƙarfafa wa mata gwiwa su fito su yi zaɓe su ma.

Ya ƙara da cewa an tanadi na’urorin auna zafin jiki, da maganin wanke hannu da bokitai saboda zaɓen.

Alalibo ya ce hukumar ta gano wuraren da ke da yiwuwar aukuwar tada hankali a lokacin zaɓen kuma ta sanar da hukumomin tsaro don a kauce wa tashin hankali.

Ya ƙara da cewa hukumar zaɓen za ta gudanar da zaɓe wanda kowa zai yi na’am da shi.

Tun da farko, sai da jagoran ƙungiyoyin masu zaman kan su, waɗanda su ke kiran kan su ‘Nigerian Civil Society Situation Room’, Mista Clement Nwankwo, ya yi bayanin cewa manufar zaman tattaunawar ita ce saboda manyan masu ruwa da tsaki a zaɓen da kwamishin zaɓen (wato Resident Electoral Commissioner, REC) su fahimci inda aka sa gaba da inda ya kamata su maida hankalin su don tabbatar da an yi zaɓe karɓaɓɓe a Edo.

Ya ce, “Mun san cewa akwai damuwa sosai game da zaɓuɓɓukan a yanzu haka, damuwa game da barazanar tashin hankali na daɗa tasowa; mu na fatan wannan zaɓe duk da fargabar da ke akwai za a yi shi cikin lumana.

“Daga ɓangaren mu na ‘yan ‘Situation Room’, mun yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, waɗanda su ka haɗa da ‘yan takara, jam’iyyun siyasa, da ma duk wani wanda ke da hannu a zaɓen, cewa akwai muhimmiyar buƙatar a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“Saboda haka mu na kira da babbar murya da a kula da zaman lafiya kuma a kula da masu zaɓe saboda idan har babu zaman lafiya to mu na da babban ƙalubale.”

Nwankwo ya ce ƙungiyoyin sun tattauna da Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, kuma ya ba su tabbacin cewa hukuma ce mai zaman kan ta wadda ba ta da wani ɗan lele a zaɓen.

Ya ce kwanan nan hukumar ta fito da wani sabon tsari inda masu zaɓe za su ga sakamakon ƙuri’un da su ka jefa da zaran an tattara su a waje guda.

Ya ce wannan sabon tsari wani cigaba ne a aikin zaɓe, wanda ƙungiyoyin sun yi murna da shi.

Ya ƙara da cewa, “Fatan mu shi ne ba za a wargaza wannan sabon tsarin ba.’’

Nwankwo ya ce ƙungiyoyin sun sa ido su ga an yi zaɓe wanda zai tabbatar da cewa an magance matsalolin da ƙungiyoyin na ‘Situation Room’ su ka damu da su game da zaɓen.

Ya ce ƙungiyoyin za su tura ‘yan sa ido mutum 300 a rumfunan zaɓen da wuraren ƙirga ƙuri’a don su ga yadda aikin zaɓen ke gudana.

Ya yi kira ga INEC da ta aiwatar da zaɓe wanda kowa zai yi murna da shi, tare da ɗaukar darussa daga babban zaɓen da aka yi a ƙasar nan a cikin 2019 kuma su inganta shi daga yanzu zuwa manyan zaɓuɓɓukan da za a yi a cikin shekara ta 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply