Zaɓen Edo: ‘Yan Takara Sun Ƙulla Yarjejeniya

‘Yan takarar kujerar gwamna daga jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar Edo da ke kudancin Nijeriya suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

Kwamitin zaman lafiya na kasa, karkashin tsohon shugaban Nijeriya, Abdussalami Abubakar ne ya shirya zaman yarjejeniyar.

Ana dai zaman dar-dar game da zaben gwamnan da za a yi a jihar, ranar asabar mai zuwa, sakamakon rashin jituwar da ake samu tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyun siyasar jihar, wato APC da PDP.

Labarai Makamanta

Leave a Reply