Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, shugaban kwamatin yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar Edo, a tattaunawar da ya yi da manema labarai, ranar Litinin a Abuja, ya bayyana cewar, Jam’iyyar PDP na son dakawa dukiyar jihar Edo wawa ne kawai.
Gandujen ya bayyana hakan ne, a harabar Sakatariyar Jam’iyyar APC bayan da aka kaddamar da kwamatin da zai jagoranta domin yakin neman zaben jam’iyyar a jihar ta Edo a zaben Gwamnan da za ai nan gaba.
Ganduje ya bayyana cewar a shirye suke su fuskanci kwamatin da PDP ta kafa karkashin jagorancin Gwamnan Ribas Nsome Wike, da zai yiwa PDP yakin neman zabe a jihar.