Zaɓen Edo: Na Kwana Ina Kuka Saboda Faɗuwar APC – Oshiomole

Tsohon shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomole ya bayyana cewa sai da ya zub da hawaye ya fashe da kuka ranar Asabar da akayi zaben gwamnan jihar Edo, inda sakamakon zaben ya nuna cewar PDP ce ta yi nasara.

A sakamakon zaben ya tabbatar da cewa gwamna Godwin Obaseki kuma dan takaran jam’iyyar PDP ne yayi nasara a zaben, da gagarumin rinjaye.

Duk da cewa jam’iyyun siyasa 14 sukayi takara a zaben, sakamakon ya nuna cewa takaran na tsakanin jam’iyyun PDP da APC ne, A cewar hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC, dan takaran jam’iyyar PDP, Gwamna Godwin Obaseki, wanda ya samu kuri’u 307,955 ya lallasa abokin hamayyarsa, Osaze Ize-iyamu wanda ya samu kuri’u 223,619.

Oshiomole na daga cikin wadanda suka yiwa jamiyyar APC da dan takararta, Ize-Iyamu yakin neman zabe.A hirarsa ta farko tun bayan zaben, Oshiomole ya bayyana yadda ya zub da hawaye yayinda ya ga tsofaffin mata sun jajirce sai sun kada kuri’arsu duk da matsalolin da aka rika samu.

Ya ce maimakon su yi fushi kan yadda na’urar tantance masu zabe ke bata lokaci, hakuri sukayi har sai da suka kada kuri’a.

Mun kawo muku cewa kwanaki uku bayan shan kashi a zaben gwamnan jihar Edo, dan takaran jami’yyar APC, Osagie Ize-Iyamu ya gana da jiga-jigan jam’iyyar biyu a Abuja.

Ize-Iyamu ya yi zaman sirri da gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwaryar APC, Mai Mala Buni, da kuma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Labarai Makamanta

Leave a Reply