Zaɓen Edo: Kar Ku Zaɓi Obaseki – Gargaɗin Tinubu

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi kira ga al’ummar jihar Edo suyi watsi da gwamna Godwin Obaseki, dake neman zarcewa kan kujerarsa.

A faifan bidiyon da tasahar TVC ta saki, Tinubu ya ce Obaseki ba jarumin demokradiyya bane kuma a yi waje da shi a zaben gwamnan ranar Asabar.

Tinubu na cikin jiga-jigan APC da suka yiwa Obaseki yakin neman zabe a shekarar 2016 karkashin jam’iyyar APC.
Amma daga baya, gwamna Obaseki ya fita daga APC zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bayan rikicin da yaki ci, yaki cinyewa tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar kuma maigidansa, Adams Oshiomole.

A jawabin da Tinubu yayi ranar Talata, Tinubu ya ce Obaseki bai yi gwagwarmayan demokradiyyan Najeriya ba.

“Ina rokonku a matsayina na dan demokradiyya kuma jagora da muyi nazari kan zaben jihar Edo kuma kuyi watsi da Godwin Obaseki,” Tinubu Yace.

“Mun sha bakar wahala wajen samar da wannan gwamnati ta demokradiyyar da muke jin dadi yanzu kuma Obaseki bai yi gwagwarmayan tabbatar da demokradiyya a kasa ba.”

“Saboda haka, ba zai fahimci daraja da wahalan dake tattare da gwagwarmaya.” “Ya bayyana halinsa na kama-karya, rashin girmama doka, da kuma rashin giramama ku mutanen da kuka zabi yan majalisar amma ya hana rantsar da su.”
“A yau, ya dawo ku sake zabenshi. Ina mai rokonku, kuyi watsi da shi kamar yadda yayi watsi da yan majalisa 14.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply