Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban riko na Jam’iyar APC na kasa Alhaji Mai Mala Buni ya kaddamar da Kwmaitin yakin zaben jihar Edo karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR tare da mataimakin sa a kwamitin wato Gwamnan jihar Imo, Hope Ozodinma da sauran ‘yan kwmaitin su 49. Za a gudanar da zaben na jihar Edo ne a ranar 19 ga watan September, 2020.
Gwamna Ganduje ya samu rakiyar Sanata Kabiru Gaya da Sanata Barau Jibrin da Hon Abubakar Bichi da Hon Lawan Kenken da shugaban jam’iyar APC na jiha Hon Abdullahi Abbas da Chief of Staff Hon Ali Haruna Makoda da Alhaji Bawuro, da Hon Kawu Sumaila.
Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
July 6, 2020