Jam’iyyar PDP ta kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jihar Edo a babban filin wasa na Samuel Ogbemudia dake jihar Edo, za a fafata zaben a ‘yan kwanaki kadan masu zuwa.
Idan ba a manta ba gwamna Obaseki na jihar edo ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jamiyyar PDP a ranar 19 ga watan yuni da ya gabata biyo bayan haramta masa takara da jam’iyyar APC tayi sakamakon takardun makarantar sa.
Yayin kaddamar da taron yakin neman zaben ne wanda akabi matakan kariya daga cutar covid 19 aka jiyo tsohon sanatan kogi ta yamma, Sanata Dino Meleye yayi wata bakarariyar addua da ta dauki hankalin mutanen wurin. Inda yace ” akwai wanda suka taso daga babban birnin tarayya Abuja da wasu jihohin kasar nan domin su murde zaben jihar Edo kamar yadda suka saba. Melaye yace ”akwai wanda suka ciko daloli a aljihun su domin su yaudari mutanen jihar Edo.
Amma mu addu’ar da za muyi shine, duk wani mai aniya ko shirin murde zaben jihar Edo Allah ya daura masa cutar sarkewar nunfashi wato korona inda mutanen wurin suka amsa da Amin…
Kuna ganin ya dace sanata Dino Melaye yayi irin wannan addu’ar?