Zaɓen 2023: Za Mu Sauya Tsarin Amfani Da Card Reader – INEC

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta ce ta fara bitar tsarin fasahar da take amfani da shi a zabuka da manufar shiga sabbin hanyoyin inganta zaben kasar kafin nan da shekara ta 2023.

”Babban daraktan yada labarai na INEC Nick Dazing ya bayyana haka a ranar Talata, lokacin wani taron karawa juna sani da sashen ya shirya domin bitar littafin wayar da kan masu zaben, wanda ya gudana a Birnin Keffi na jihar Nasarawa.

”Da yake magana da ‘yan jarida kan muhimmancin taron wanda hukumar ta shirya hadin guiwa da Gidauniyar ‘Westminster Foundation for Democracy’, Dazing ya ce INEC ta fara amfani da kwamfuta lokacin zabe tun a shekarar 2004, kuma tana ci gaba da inganta tsarin don ya dace da zamani.

Kuna ganin wannan tsari zai kawo rage magudin zabe a kasar mu Najeriya?

Labarai Makamanta