Zaɓen 2023: Wasu ‘Yan Najeriya Sun Fara Zawarcin Jonathan

Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, an rawaito cewa wasu ‘yan Najeriya na duba yiwuwar marawa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan baya don darewa kujerar Shugabancin kasa bayan kammala wa’adin shugabancin shugaban kasa Buhari.

A cewar rahoton, ‘Yan Najeriya da ke wannan tunani waɗanda wasu makusantan shugaba Buhari ne, na ganin cewa Jonathan ne mutumin da ya fi dacewa da wannan matsayin idan har za a mika shugabancin kasar ga yankin kudu.

“Ya mika mulki cikin lumana sannan bai kullaci kowa da mugun nufi ba saboda haka ba zai zama barazana ga ra’ayin arewa ba.”

Wani dalili da yasa wadannan masu biyayya ga Buhari ke duba yiwuwar marawa shugabancin Jonathan baya a 2023 shine cewa zai yi mulki ne na zango daya. Wato shekaru hudu kawai, wanda hakan ke nufin mulki zai dawo arewa cikin dan kankanin lokaci.

A cewar masu wannan tunani, idan har wani dan kudu ya yi nasara, yana iya shafe shekaru takwas a kan mulki kafin ya dawo ga arewa.

ZaA cewar wadannan majiyoyi, tsawon shekaru da suka gabata, Buhari da magoya bayansa na kallon tsohon shugaban kasar a matsayin amintacce wanda za a iya dogaro da shi. Sun bayyana cewa Jonathan ne kadai tsohon Shugaban kasa da ya kasance tare da Buhari a lokacin bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai a Eagle Square, Abuja.

Labarai Makamanta