Mamman Daura, dan uwa shakiki sannan kuma makusanci ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shawarci ‘yan Najeriya a kan su zabi dan takarar da ya fi dacewa a zaben kujerar shugaban kasa a shekarar 2023.
Daura ya bayyana hakan ne yayin daya daga cikin daidaikun hirar da ya yi da sashen Hausa na radiyon BBC wacce aka yi ranar Talata a Abuja.
A cewarsa, tunda Najeriya ta gwada tsarin karba – karba har sau uku a baya, zai fi dacewa yanzu jama’a su bawa cancanta fifiko a shekarar 2023, su manta da yankin da mutum ya fito.
Ya ce yin hakan zai inganta hadin kai a cikin kasa.
Da aka tambayeshi a kan alakarsa da shugaban kasa Buhari, sai ya ce; “Kawuna ne, kanin mahaifina ne. Mahaifina aka fara haifa, shi kuma Buhari shine dan auta.”
Kazalika, an sake tambayar Mamman Daura ko da gaske ne cewar tare suka taso da shugaba Buhari, sai ya kara da cewa, “wannan gaskiyane, tare mu ka taso.”
Tun bayan da Shugaba Buhari ya dare kan mulki a shekarar 2015, rahotanni da dama da aka wallafa sunyi ikirarin cewa Daura yana daga cikin tsirarin mutanen da ake yi wa lakabi da ‘cabal’ da aka ce su ke juya akalar gwamnatin Buhari.
Amma, yayin hirarsa da ya yi da BBC Hausa a ranar Talata, Daura ya ce shawara kadai ya ke bawa Shugaba Buhari amma ba ya tilasta masa ra’ayoyinsa ko fada masa abinda zai yi.
Da akai masa tambaya kan cewa ko yana gana wa da Shugaba Buhari domin bashi shawarwari a kan harkokin da ke faruwa a Najeriya, Mamman Daura ya bayar da amsa kamar haka; “Eh, na kan ziyarce shi domin in gaishe shi.”
“Na kan bashi shawara amma idan ya tambaya … Amma bana zuwa domin kashin kaina ko na tilasta masa wani abu. A’a; Ba a yi wa gwamnati haka.”