Jam’iyyar APC ta musanta rade-radin da ke cewa tana zawarcin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya yi mata takara a zaben 2023.
A makon da ya gabata ne wasu rahotanni suka bayyana cewa gwamnonin Arewa na aiki tukuru kan ganin Jonathan ya dawo APC.
Sai dai shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni, ya ce “Na san mutane za su yi zargin haka saboda ziyarar da muka kai wa Jonathan lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.
“Ziyarar na da alaka ne kawai a matsayinsa na tsohon Shugaban Kasa; babu wata magana mai kama da takarar da zai yi mana.
“A siyasa muna ziyartar junanmu duk lokacin da wani abu ya same mu na jaje ko murna.”
Buni ya bayyana haka ne yayin da yake tatraunawa da Sashen Hausa na BBC, inda ya ce babu wani abu mai kama da takarar Jonathan a APC.
Buni, wanda shi ne Gwamnan Jihar Yobe, ya ce matsayin Jonathan na tsohon shugaban kasa kuma mai kaunar zaman lafiya, wajibi ne a martaba shi.
“Idan ana neman mutum mai son zaman lafiya, to ya kamata a martaba Jonathan saboda yadda ya amince da faduwa zabe a 2015.
“Don haka ya kamata a rika karrama shi a matsayin uban kasa,” inji Buni.