Zaɓen 2023: INEC Za Ta Shigo Da Sabbin Dabarun Hana Maguɗi

Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Nijeriya, ta ce tana sake duba fasahohin da ake amfani da su.

Hukumar ta bayyana cewa tana yin wannan aiki ne da nufin kawo sababbin kirkire-kirkire da su inganta sha’anin zabe nan da shekarar 2023.

Daraktan da ke kula da wayar da kan masu zabe da yada labarai, Nick Dazang, ya bayyana haka wajen wani taron karawa juna sani a Keffi, jihar Nasarawa.

Lamarin zaɓen Shekarar 2023 shine babban abin da ke ɗaukar hankulan jama’a a halin yanzu a Najeriya, inda ake cigaba da tafka mahawara akan sashin da zai fitar da shugaba bayan kammala wa’adin mulkin Buhari.

Da yawan Jama’ar Arewa na ganin ayi watsi da tsarin karɓa-karba a koma ainihin tafarkin dimukuraɗiyya da ke bada dama kowa ya fito ya jarraba sa’arshi.

Labarai Makamanta