Jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta karyata zargin cewa tayi watsi da dan takaranta a zaben shugaban kasan 2019, Atiku Abubakar, domin zaben wani a 2023.
Shugaban uwar jam’iyyar, Uche Secondus, ya karyata labarin bayan ganawarsa da wasu gwamnonin jam’iyyar a Bauchi.
Secondus ya ce jam’iyyar za ta tabbatar da cewa duk wanda ya cancanci takara zai iya ba tare da tsangwama ba.
“Wannan jam’iyyar tana abubuwanta a demokradiyyance ne, babu nuna wariya. Duk wanda ya cancanta, tsoho ko yaro, gwamna ko tsohon gwamna, zai samu daman takara.”
Wadanda suka halarci zaman sune mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa, Sanata Nazif Suleiman Gamawa, da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Hakazalika akwai gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Gombe, Hassan Ibrahim Dankwambo.
Gwamnan jihar Bauchi, AbdulKadir Bala, ne ya karbi bakuncinsu.