An bayyana cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari a zaɓen shekarar 2015 duk da cewa ya san ‘bai san komai ba’ kuma ba zai iya gudanar da Shugabanci ba, amma ya yi haka ne, saboda rashin gamsuwa da salon Mulkin Jonathan.
Tsohon gwamnan jihar Osun Mista Olagunsoye Oyinlola ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai. Ya ƙara da cewa Mista Obasanjo ya yanke shawarar goyon bayan Buhari ne saboda takaicin gwamnatin Goodluck Jonathan.
“Duk da cewa (shi) Obasanjo ya san cewa dan takarar na jam’iyyar APC Buhari ba zai iya tabuka wani abin azo-a-gani ba, amma duk da haka ya goyi bayansa bayan wasu jiga-jigan ‘yan Najeriya sun matsa masa lamba.
Mista Oyinlola, wanda ya taba rike mukamin sakataren jam’iyyar PDP na kasa, ya yi wannan jawabin ne a wata hira da ya yi da The Punch.
“Mutum na karshe da ya amince da Buhari shine Obasanjo kuma ina da tabbacin haka saboda ina cikin tawagar. Eh, Baba (Obasanjo) ya samu matsala da Jonathan. A lokacin zai amince da kowanne zabi amma banda Jonathan,”.
“Idan aka yi la’akari da ‘yan takarar da sauran jam’iyyun suka tsayar, babu wanda zai iya mulkar Najeriya fiye da yadda Buhari zai yi a lokacin. Shi yasa aka goyi bayan Buhari.
“Bayan haka, duba da cewa ya taba rike shugabancin kasar a karkashin mulkin soja, don haka ya fi sauran ta wannan bangaren. Amma Baba Obasanjo shine na karshen amincewa ya marawa Buhari baya.”
Oyinlola ya ce shi da su Saraki, Amosun, Bola Tinubu, Kashim, Imam suka tafi wurin Baba (Obasanjo) a gonar Ota da karfe bakwai na safe kafin ya amince.