Hukumar Yan’sanda ta rufe Iyakokin Jihar Bauchi, ta rufe iyakokin Jihar don gudanar da zaben kananan hukumomi a dukkannin fadin Jihar daga 12 na daren jumma’a zuwa karfe 2 na ranar Asabar 17 ga watan Oktoban 2020.
Kwamishinan yan’sanda Lawal Tanko Jimeta ya shaida hakan ga manema labarai kan samarda tsaro a zaben na yau.
Tanko Jimeta yace wadanda suke da ruwa da tsaki ne kawai doka ta bari suyi zurga-zurga a yayin gudanar da zaben domin.
“Baza mu yadda da yawo daga wanchan wuri zuwa wanchannwuri ba domin tabbatar doka da oda, don gudun kar wasu su fake da zaben su kawo rudani, yace duk wanda muka kama to ya kuka da kansa”
Kana shugaban Yan’sandan ya ja hankalin masu rike da mukamai na gwamnati da suje rumfar zabe ba tare da, jam’ian tsaron su ba.
Haka nan yace, zasu yi aiki kafada da kafada da sauran jami’an tsaro lungu da sako, don tabbatar da anyi zabe mai inganci.
Jimeta, akarshe yace shuwagabbanin al’ummah da na addinai da masu rike da sarautun gargajiya dana matasa da suyi kira da zaman lafiya lokacin gudanar da zaben.