Yunwa: Gwamnatin Tarayya Ta Amince A Shigo Da Shinkafa Da Sauran Kayayyakin Abinci Daga Waje

images 2024 03 14T070645.613

Gwamnatin tarayya ta amince da shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa wake da alkama da sauran kayayyakin masarufi a fa?in ?asar.

A wani taron manema labarai da ya kira wannan Litinin, ministan noma da samar da abinci na Najeriya, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana hakan, inda ya ce shugaba Tinubu ya amince da janye ?udin fito kan muhimman kayan abincin ne har tsawon kwanaki 150, domin neman wadatuwar kayan a Najeriya.

?an Najeriya dai na fama da tsa?ar kayan abinci tun bayan da shugaban ?asar ya bayyana janye tallafin man fetur a bara tare da ?arya darajan ?u?in ?asar Naira ta yadda kasuwa za ta yi halinta kan ?u?aden ?asashen waje.

Manufofin sun haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da ?asar ta da?e bata irinsa ba, inda farashin shimkafa mai nauyin 50kg ya haura Naira dubu 70 daga kimanin N20 da yake kafin ?arewar tinubu mulki.

Masharhanta da wasu ?an Najeriya sun yi kira ga shugaban ?asar da ya bari a shigo da kayan abinci daga ?asashen waje domin dakile tashin farashin kayayyakin abinci, amma masu adawa da matakin sun ce hakan zai shafi manoman cikin gida.

Gwamnati za ta shigo da alkama da masara daga waje
Sanarwar ta ce baya ga janye ?u?in fito ga ?an kasuwa masu bukatar shigo da kayan abinci, ita kanta gwamnatin tarayya za ta shigo da alkama kimanin tan dubu 250 da masara shima tan 250, za’a baiwa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.

Related posts

Leave a Comment