Yunkurin Masari Na Rabon Gidaje Ga ‘Yan Bindiga Kuskure Ne – Sani

Tsohon dan Majalisa wanda ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa Sanata Shehu Sani, ya soki lamirin Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina a kan yunkurin rarrabawa tubabbun ‘yan bindiga gidaje da shaguna.

A yayin martani ta shafinsa na Twitter, Sanata Sani, ya ce wannan kawai hanya ce ta gwangwaje masu laifi. Kamar yadda yace, wannan karamcin zai kara fadada laifuka tare da kara bai wa wasu kwarin guiwa.

“Gwamnatin jihar Katsina tana kokarin bai wa ‘yan bindiga gonaki, shagunan kasuwa da gidaje wanda hakan hanya ce ta karrama ‘yan ta’adda.

“Hakan kuwa zai kara musu karfin guiwa tare da bai wa wasu sha’awar shiga harkar. Zai kara tsananta matsalar tsaro a yankin arewa,” inji Shehu Sani.

Idan za mu tuna, Masari a ranar Laraba ya fara bayanin yadda za a bi da ‘yan bindiga ta hanyar basu gidaje, shagunan kasuwanni da gonaki ga duk wanda zai ajiye makamai domin tabbatar da wanzuwar tsaro a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce gwamnatin jihar ta kammala shirinta na karbar tubabbun ‘yan bindiga kuma za ta basu muhalli.

“Wannan yana daga cikin shirin gwamnatin na gyara dajin Rugu kuma ta bai wa tubabbun ‘yan bindigar.
An kafa kwamiti domin samar musu da ababen more rayuwa.

“Wasu daga cikin yankunan sun hada da dajin yankin Yantumaki da Maidabino da kuma dajin Sabuwa da Faskari,”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply