Gwamnatin jihar Yobe za ta dauki matasa 250, ‘yan asalin jihar aikin jami’an kula da zirga-zirga (YOROTA).
A ranar Litinin ne ake sa ran za a bude yanar gizo domin daukar aikin, kuma ana tsammanin zuwa ranar Talata 20 ga watan Agustan shekarar 2020 za a kulle.
Karkashin adireshin yanar gizo kamar haka: www.yorota.yb.gov.ng
Takardar sanarwar ta fito daga ofishin babban manajan YOROTA na jihar, Alhaji Bature.