Labarin dake shigo mana daga jihar Yobe na bayyana cewar Alhaji Bashir Machina, halastaccen ‘dan takarar kujerar Sanata a jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa yace nasararsa a kotu akan Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan daga Allah ne.
A yayin gangamin zagayawa tare da mika godiya ga magoya bayansa, Lawan yace duk wanda zai kare hakkin jama’arsa dole ya ga kalubale Machina ya dauki alkawarin Tafiya da dukkan kananan hukumomi shida dake karkashin mazabarsa idan ya samu nasara a babban zaben dake tafe.
Machina wanda ya bayyana hakan a Nguru dake jihar Yobe a wata liyafa da gangamin mika godiya ga magoya bayansa, yayi bayanin cewa duk wanda ke yaki domin hakkin mutanensa dole ne ya fuskanci kalubale.
Zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 28 ga watan Mayu a Yobe ta arewa a watannin nan ya fuskanci kalubale mai tarin yawa wanda ya kawo hargitsi har aka kai ga danganawa da kotu tsakanin Machina da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.
Sanata Ahmed Lawan ya kwashe shekaru 20 yana wakiltar mazabarsa ta Yobe ta arewa a majalisar dattawa kafin Machina ya kwace kambunsa tun a zaben fidda gwani.