Yobe: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Dukkanin Kananan Hukumomin Jihar

IMG 20240229 WA0098

Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 17 da aka kammala zaben kananan hukumomin jihar.

Haka kuma jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun kansiloli 178 na jihar.

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Yobe, YOSIEC, Dr Mamman Muhammad, ne ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar da ke Damaturu a ranar Lahadi.

“APC ta lashe dukkan kujeru 17 da kansiloli 178 a zaben kananan hukumomin jihar,” in ji shi.

Ya kara da cewa hukumar ta karba, ta duba, ta tantance tare da amincewa da sakamakon kowanne daga cikin kansiloli 178 da suka samu.

Dr. Muhammad ya yabawa masu zabe bisa tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

An gudanar da zaben ne ba tare da halartar jam’iyyar, PDP ba.

Jam’iyyar ta bakin sakataren kungiyar Mohammed Sulayman a baya ta yi ikirarin cewa mai yiwuwa zaben bai kasance cikin gaskiya da adalci ba.

Related posts

Leave a Comment