Gamayyar ƙungiyoyin fafutukar kwato ‘yancin bil’adama sun bayyana aniyarsu na maka Gwamnatin Nijeriya gaban kuliya a kan irin yadda ake ta ciyo wa kasar bashi kuma ba a ganin inda ya shiga duk da haka ana ta kara rakito wani bashin.
Gamayyar kungiyoyin 40 dai sun fitar da sanarwar hakan ne bayan kammala wani taron tattaunawa a tsakaninsu da suka yi a birnin Legas.
Gamayyar sun kuma zabi sababbin shugabanni a zaman da suka yi inda suka zabi Kwamared Shetima Yerima ya zama shugaban tafiyar.
Gamayyar kungiyoyin sun dai bayyana cewa kungiyoyi ne daga kowane bangare na tarayyar Nijeriya Kudu, Arewa, Kusu Maso Gabas da Kudu Maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas , tsakiya da Arewa maso Yamma duk akwai fitattun kungiyoyi kamar yadda shugaban ya bayyana.
Kamar yadda ya ce ” Fitattun kungiyoyi ne ba muna kungiya ba shi ne aka hada su aka samu kungiya guda 40 da za a yi wannan fafutukar da su”.
Kwamared Shetima Yarima ya ci gaba da cewa akwai matsalar rashin tsaro a kasar ga batun cin hanci da rashawa, satar mutane da yi yawa musamman a yankin arewacin Nijeriya zai yi wahala a samu awa daya baka ji an sace mutum ba, wannan lamari yana samun jama’a kwarai.
Da yake amsa tambaya a kan cewa ba suna siyasa bane ta yadda wasu suke amfani da su sai ya amsa tambayar da cewa ” Dukkan mu nan ba yara bane don haka mun fi karfin wani ko wasu suyi amfani samu, kawai fafutuka ce domin kwato yanci da samun maganin matsalolin da ke damun kasar”. Inji Yarima.
“Za mu samar da wadansu kwamitocin da za su je su zauna domin tattaunawa da dukkan wadansu al’ummomin da suke fama da wata matsala a tsakaninsu domin warware ta baki daya, a samu ci gaban kasa da jama’arta daya.