‘Ya’yana Hu?u CORONA Ta Yi Wa Mummunan Kamu – Boss Mustapha

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustpha, ya ce ‘ya’yansa hudu ne suka kamu da muguwar cutar korona, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona, ya sanar da hakan ne a wani bayani da yayi a Abuja a ranar Litinin.

Ya ce daga cikin iyalinsa da cutar ta kama har da yaro mai shekara daya.

Sakataren gwamnatin tarayyan ya killace kansa a makon da ya gabata sakamakon mu’amala da yayi da masu cutar.

Ya ce a yayin da shi da matarsa suka bayyana basu dauke da cutar, ‘ya’yansa a halin yanzu suna jinya.

Related posts

Leave a Comment